Ban da wannan kuma, Mr. Sy ya kara da cewa, a shekarun baya, yawan yaran da aka gana musu azaba, ciki har da gana musu azaba ta fuskar jima'i na ta karuwa. A yawancin lokaci, irin wannan lamari ya auku a cikin iyalai da unguwanni, ta haka asusun UNICEF da unguwanni sun hada kai, su yi kokarin kyautata tunanin mutane kan kiyaya hakkokin yara da yayata da'ar kulawa da yara sosai. Sa'an nan kuma, asusun UNICEF ya zura ido kan halin da kasashen Afirka suke ciki a harkokin dokoki, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su tsara dokoki domin kare hakkokin yara.
Yake-yaken da aka samu a Afirka sun haifar da dimbin 'yan gudun hijira da kuma wadanda suka rasa wurin kwana. Bisa kididdigar da asusun UNICEF ya yi, an ce, a cikin wadanda suka bar garinsu, kimanin rabinsu yara ne. Mr. Sy ya ce, abu mafi muhimmanci domin taimakawa wadannan yara shi ne yin rigakafin aukuwar rikici, da inganta ayyukan yayata da ba da ilmi kan muhimmancin zaman lafiya, ta haka kasashen duniya da 'yan kabilu daban daban za su iya yin zaman tare cikin jituwa. Yaran da suke zama a sansanonin 'yan gudun hijira fa, asusun UNICEF ya dauki matakai da yawa domin tabbatar da ganin sun ci gaba da samun ilmi da allurar rigakafi da kuma magani.
A karshen zantawar, Mr. Sy ya ci gaba da cewa, wani abun gaskiya da ba za a iya kyalewa ba shi ne ya zuwa yanzu Afirka wata nahiya ce da ke fuskantar matsaloli mafi yawa, kuma kusan wadannan matsaloli sun yi illa ga rayuwar yara a duniya a wurin. Dadin dadawa kuma, matsaloli da yawa da kasashen duniya ke fuskanta, kamar sauyawar yanayi da matsalar kudi ta duniya, su ma sun kawo wa yara illa ta fuskar rayuwarsu a duniya da kuma bunkasuwarsu. Saboda haka, kasashen duniya na sauke nauyin kawo wa yara alheri. Ya kamata su yi alkawari a hukumance kan kiyaye hakkokin yara.(Tasallah)