Mista Wu ya ce, babban taken taron da aka yi a ranar 14 ga wata da maraice shi ne "inganta mu'amala a wannan yanki", inda aka yi tattaunawa mai zurfi kan 'yantar da harkokin ciniki a yankunan Asiya da Pacific, da bude kasuwanni da sauransu, haka kuma an cimma sakamako mai kyau tsakanin bangarori daban-daban.
A waje guda kuma, shugabanni mahalarta taron sun cimma matsaya kan nuna adawa ga kowane irin ra'ayin bada kariya ga harkokin ciniki, haka kuma sun sake jaddada alkawarin da suka dauka na cewa, ba za su kafa sabon shinge ba ga harkokin ciniki da zuba jari, kuma za su duba wannan batu lokaci-lokaci.(Murtala)