Shugaba Hu Jintao ya soma ziyararsa ne tun daga ranar 10 ga wata. Tuni, a karo na farko ya yi ziyarar aiki a kasashen Malasiya da Singapore. Daga ranar 14 zuwa 15 ga wata, a kasar Singapore, Hu Jintao ya halarci kwarya-kwaryan taro a karo na 17 tsakanin shugabannin kasashe membobin kungiyar APEC, inda ya bayyana ra'ayoyi da matsayin da gwamnatin kasar Sin ke tsayawa a kai dangane da batutuwa da dama, ciki kuwa har da tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya, da farfado da tattalin arzikin duniya, da nuna goyon-baya ga bunkasuwar tsarin yin ciniki na bangarori daban-daban, gami da inganta hadin-gwiwar sassa daban-daban da sauransu.(Murtala)