A wannan rana, Mr. Hu Jintao ya halarci zagaye na biyu na taron kwarya-kwarya na shugabannin kungiyar APEC karo na 17 da aka yi a kasar Singapore, kuma ya bayar da wani muhimmin jawabi.
A cikin jawabinsa, Mr. Hu ya shawarci kungiyoyin tattalin arziki daban daban da su dauki kwararan matakai masu amfani da kuma kara mai da hankali kan yadda za a sa kaimi ga mutanen da su kara kashe kudi da raya bukatun da ake da shi a kasuwannin cikin gida. Sannan dole ne a tsaya tsayin daka kan matsayin tabbatar da ganin an yi cinikayya da zuba jari a duk duniya cikin 'yanci kuma cikin daidaito ba tare da kowane irin shinge ba domin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba daga dukkan fannoni. Sannan a lokacin da ake farfado da tattalin arziki, ya kamata a kyautata tsarin makamashin da ake amfani da shi da kyautata tsarin sana'o'i da kuma kara karfin raya tattalin arzikin bola jari domin neman ci gaba ba tare da tangarda ba. (Sanusi Chen)