in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin hadin-gwiwa ta Zimbabwe tana ci gaba da duba yadda rikici ke gudana tsakanin bangarori daban-daban
2009-11-12 21:18:00 cri
Kwanan baya, a Maputo, babban birnin kasar Mozambique, kungiyar raya kudancin Afirka SADC ta shirya wani zaman taro tsakanin shugabannin wasu kasashe, inda aka samu nasarar daidaita rikici tsakanin sassa daban-daban a gwamnatin hadin-gwiwa ta Zimbabwe, da bukatar manyan shugabanni uku daga gwamnatin da su gudanar da shawarwari nan da kwanaki 15 dake tafe, gami da warware dukkanin matsaloli a cikin kwanaki 30.

Manazarta daga kasar ta Zimbabwe sun nuna yabo ga muhimmiyar rawar da kungiyar SADC ke takawa a fannin daidaita rikici, amma suna nuna damuwa sosai kan yadda za'a kawar da bambanci daga dukkan fannoni cikin wani kankanin lokaci.

A watan Maris na bara, an shirya zabubbukan shugaba, da 'yan majalisar dokoki, gami da kananan hukumomi a Zimbabwe, lamarin da ya haifar da mummunan rikicin siyasa a kasar. Sakamakon kokarin shiga-tsakani da kasa da kasa suka yi, musamman ma kungiyar tarayyar Afirka da kungiyar raya kudancin Afirka, shugabannin manyan jam'iyyun siyasa uku a kasar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar raba madafun iko a birnin Harare a watan Satumban bara. Har wa yau kuma, bisa wannan yarjejeniya, a watan Fabrairun bana, an kafa gwamnatin hadin-gwiwa ta Zimbabwe dake karkashin jagorancin shugaban kasar Robert Mugabe, da firaminista Morgan Tsvangirai, gami da mataimakin firaminista Arthur Mutambara.

Amma a ranar 16 ga watan Oktoban bana, ba zato ba tsammani firaminista Morgan Tsvangirai ya sanar da cewa, jam'iyyar MDC dake karkashin jagorancinsa ta yanke shawarar janyewa daga cikin gwamnatin hadin-gwiwa, dalilin kuwa shi ne, yana tsammanin jam'iyyar ZANU-PF dake karkashin jagorancin Robert Mugabe ta dage aiwatar da yarjejeniyar yin sulhu ta fannin siyasa da gangan.

Abun da Tsvangirai ya yi ya jawo hankalin kasashen duniya, har ma akwai wasu gwamnatocin kasashen yammacin duniya, da kafofin watsa labarai, da kungiyoyin da ba na gwamnati ba wadanda suka sake kururuta matsalolin Zimbabwe, da ci gaba da yin suka kan batun kare hakkin bil'adama na gwamnatin Mugabe.

A hakika, tun kafuwar gwamnatin hadin-gwiwa ta Zimbabwe, Robert Mugabe da jam'iyyarsa ta ZANU-PF sun yi kira ga kasashen yammacin duniya da su soke takunkumin da suke sanyawa kasar, da bukatar jam'iyyar MDC da ta kalubalanci kasashen yammacin duniya su cire takunkumi bisa yarjejeniyar yin sulhu ta fannin siyasa.

A waje guda kuma, kafa gwamnatin hadin-gwiwa da aka yi na samar da alheri ga jama'ar kasar Zimbabwe, wadanda suke fama da tashin hankali da ya ki ci ya ki cinyewa. A halin da ake ciki yanzu, masana'antu, da ayyukan gona, da kasuwanni na Zimbabwe suna farfadowa, haka kuma ana kokarin farfado da imanin masu zuba jari da masu yawon shakatawa daga kasashen ketare.

Manazarta suna ganin cewa, sanar da janyewa daga gwamnatin hadin-gwiwa da jam'iyyar MDC dake karkashin jagorancin Tsvangirai ta yi, ba ma kawai zata rasa samun goyon-baya daga jama'ar kasar ba, har ma shugabannin kasashe daban-daban a wannan yanki suna nuna damuwa sosai kan wannan batu. Ana iya ganin cewa, taron da aka yi a wannan karo a birnin Maputo ya ci gaba da yin kira ga kasa da kasa da su cire takunkumin da suke sanyawa Zimbabwe ba tare da bata lokaci ba, da bukatar manyan shugabannin gwamnatin hadin-gwiwa ta kasar da su nuna hazaka wajen daidaita matsalolin kasar.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China