To, mun gode, malam Mohammed Idi Gargajiga daga tarayyar Nijeriya. Lalle, zaman taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa zai ba da taimako wajen kara karfafa zumunta da kuma hadin gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. Bayan haka kuma, malam Gargajiga, kada ka damu, malama Lubabatu tana cikin koshin lafiya, kuma tana samun wani kwas na tsawon watanni 3 domin kara ilmi. A sabili da haka, nan ba da dadewa ba, malama Lubabatu za ta dawo ta ci gaba da gabatar muku da shirye-shirye masu kyau. To, ni fa, zan kara kokari domin samun karbuwa. Allah ya kara taimakawa.
To, sakon malam Mohammed Idi Gargajiga ke nan. Bayan haka, kwanan nan, wani mai sauraronmu a kullum malam Ladan Nasidi a kasar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Na yi imani cewa, wannan taro zai ba da damar musayar ra'ayoyi masu ilimantarwa tare da taimakawa tattalin arzikin kasashen Afirka, wadanda ke fama da masifu da talauci da cututtuka da suka addabi Nahiyar. Ina fatan kasar Sin a matsayinta na wata kasar dake kan gaba a fannin tattalin arziki a duniya za ta taimakawa kasashen Afirka har ma da sauran kasashen duniya kamar yanda take yi a halin yanzu. Allah ya kara karfafa dankon zumunci tsakanin Najeriya da kasar Sin."
To, mun gode, malam Ladan Nasidi daga Nijeriya. Mu ma mun yi imani da cewa, zumunta da amincewa da juna tsakanin Sin da kasashen Afirka za su kara zurfafa a yau da kullmu. Bayan haka, malam Shaihu Usman a kaduna, tarayyar Nijeriya yayin wata tambaya cewa, "Don Allah, ku ba ni cikakken bayani kan tarihin shugaban Amurka Barack Obama." To, za mu kokarta amsa wannan tambaya, da fatan malam Shaihu Usman kana sauraronmu a yanzu.
An haifi Barack Obama a ran 4 ga watan Agusta na shekarar 1961 a birnin Honolulu, hedkwatar jihar Hawaii ta kasar Amurka. Mahaifinsa wani dalibi ne daga kasar Kenya, kuma mahaifiyarsa mutumiyar jihar Kansas ta kasar Amurka. A yayin da suke karatu a jami'ar Hawaii, suka gamu da juna. Daga bisani, mahaifinsa ya shiga jami'ar Harvard domin samun ilmi. A sakamakon haka, Barack Obama ya girma tare da mahaifiyarsa. Yayin da shekarunsa suka kai 2 a duniya, auren dake tsakanin mahaifansa ya kare. Daga baya, Barack Obama mai shekaru 6 da haihuwa ya fara zamansa tare da mahaifiyarsa da mijinta na biyu a kasar Indonesia.
Bayan shekaru 4 da suka gabata, Barack Obama ya koma jihar Hawaii. Bayan da ya kammala karatunsa a makarantar midil, ya shiga kwalejin yamma na jihar California domin samun ilmi, daga bisani ya shiga jami'ar Colombia dake birnin New York na kasar Amurka. A shekarar 1983 ya kammala karatunsa. Daga bisani, bayan shekaru 2, wato a shekarar 1988, Barack Obama ya shiga jami'ar Harvard domin koyon ilmin dokoki. A shekarar 1991, bayan da ya samu digiri na uku, Obama ya zama wani lauya a birnin Chicago.
Bayan haka, a shekarar 1997, Barack Obama ya shiga dandalin siyasa inda ya zama wani dattijo na jihar Illinois. A watan Nuwamba na shekarar 2004, ya zama wani dattijo na tarayyar Amurka. A daidai wannan lokaci, ya tsara kudurin sarrafa makamai, da sa kaimi ga jama'a da su sa ido kan asusun tarayya, da nuna goyon baya ga jerin kudurori dangane da yakin neman zabo da magudi cikin zabe da sauyawar yanayi da dai sauransu. Dadin dadawa, Barack Obama ya kai ziyara a wasu kasashe dake gabashin Turai da yankin Gabas ta tsakiya da kuma wasu kasashen nahiyar Afirka.
A watan Feburairu na shekarar 2007, Barack Obama ya sanar da niyyarsa ta shiga takarar matsayin shugaban kasar Amurka a hukunce. A cikin jawabinsa, ya jaddada bukatar kawo karshen yakin Iraki, da samar da makamashi da kanta, da dakatar da manufar rage kudin haraji, da tabbarar da ishorar kiwon lafiya da sauransu. Kuma ya alkawarta tabbatar da hadin gwiwa tsakanin jam'iyyu, da sake kafa dangantakar abokantaka da kasashen duniya, da maido da matsayin Amurka na yin jagoranci. A ran 4 ga watan Nuwamba na bara, ya cimma nasara a babban zaben shugaban kasa, ya zama shugaban Amurka na 56, kuma shugaba ne na farko mai asali a Afirka a tarihin kasar. A ran 20 ga watan Janairu na bana, Barack Obama ya yi rantsuwar kama aiki. A ran 9 ga watan Oktoba, kwamitin kula da lambar yabo ta Nobel ya ba shi lambar yabo ta Nobel ta shimfida zaman lafiya ta shekarar 2009, a yunkurin yabawa kokarinsa a game da karfafa hadin gwiwa tsakanin jama'a da harkokin waje tsakanin kasa da kasa.
To, jama'a masu sauraro, yanzu bayani ke nan kan tambayar malam Shaihu Usman a kaduna, tarayyar Nijeriya, da fatan ka ji ka gamsu da shi. Bayan haka, kwanan nan, masu sauraronmu da dama sun aiko mana da wasiku, a ciki har da malam Namadina Yahya a Dakar dake Senegal, da malam Maman Yawale, a Niamey, kasar Nijer, da malam Bello Gero, a sokoto, tarayyar Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba, sabo da karancin lokaci. Don haka muna farin ciki, da fatan za ku ci gaba da sauraron tashar CRI. To, jama'a masu sauraro, yanzu shirinmu ke nan, ni Fatima ke cewa da alheri daga nan gidan rediyon kasar Sin.(Fatima)