To, mun gode, malam Is'haq Abdul-Hadi Bashir, a garin Zariya na jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. Bayan karanta sakonka, muna matukar farin ciki sabo da kokarinka na koyon Sinanci. Muna fatan ka samu babban sakamako kuma mai kyau a wannan fanni. Ba shakka za ka more a nan gaba. Allah ya kara taimakawa.
To, sakon malam Is'haq Abdul-Hadi Bashir ke nan. Bayan haka kuma, malam Sabo Bawa Bako daga jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Ina son amfani da wannan dama in yi wa daukacin musulman duniya da na kasar Sin fatan alhairi, da fatan za a yi salla lafiya."
Mun gode, malam Sabo Bawa Bako daga jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya, da fatan kai ma ka yi salla lafiya. Bisa kokarinmu, zumunta dake cikin zukatanmu za ta karfafu yadda ya kamata.
Kwanan nan, malam Hamissou Abdou, daga katsina, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "Don Allah, ku ba mu cikakken bayani kan dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka." To, yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya, da fatan malam Hamissou Abdou kana sauraronmu a yanzu.
Bayan shiga sabon karni na 21, shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwa sun zama burin jama'ar kasa da kasa baki daya. Bisa shawarar da wasu kasashen Afirka suka bayar, a watan Oktoba na shekarar 1999, gwamnatin kasar Sin ta ba da shawarar kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da taron ministoci a birnin Beijing a shekarar 2000, a yunkurin karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin hali mai kyau, da tinkarar kalubalen da aka gamu da shi a lokacin raya tattalin arzikin duniya bai daya, da kuma neman bunkasuwa tare. A sabili da haka, kasashen Afirka sun mai da martani da kuma nuna goyon baya ga wannan shawara cikin yakini.
Bisa kokarin Sin da Afirka, kawo yanzu dai, an riga an gudanar da tarurrukan ministoci sau uku na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.
Daga ran 10 zuwa ran 12 ga watan Oktoba na shekarar 2000, an yi taron ministoci a karo na farko na dandalin tattaunawar a birnin Beijing na Sin, inda aka yi shawarwari kan "Yadda za a sa kaimi ga kafa sabon tsarin tattalin arziki da na siyasa na duniya a sabon karni na 21", da "Yadda za a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da cinikayya a cikin wani sabon yanayi mai kyau", bisa ka'idojin yin shawarwari masu adalci, da kara yin musayar ra'ayi da fahimtar juna da kuma sada zumunta, da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu. A gun taron, an zartas da "Sanarwar dandalin tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a birnin Beijing", da "Tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma", wadanda suka tabbatar da hanyar bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka mai adalci cikin dogon lokaci. Dadin dadawa, a yayin wannan taro an yi tarurrukan karawa juna sani 4, wadanda suka shafi zuba jari da cinikayya tsakanin Sin da Afirka, da musanyar fasahohin yin kwaskwarima da rage talauci da kuma bunkasa aikin gona mai dorewa, da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannin tarbiyya da kimiyya da fasaha da kiwon lafiya da dai sauransu.
Bayan haka, daga ran 15 zuwa ran 16 ga watan Disamba na shekarar 2003, an gudanar da taron ministoci a karo na 2 na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha. A gun taron, an yi shawarwari kan sabbin ra'ayoyi da matakan da za a dauka wajen karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a muhimman fannonin aikin gona da manyan ayyuka da zuba jari da cinikayya da dai sauransu. Kuma an zartas da "Shirin Addis Ababa na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka daga shekarar 2004 zuwa shekarar 2006". Bugu da kari, an gudanar da taron shugabannin kamfanonin Sin da Afirka a karo na farko. Masu kula da harkokin masana'antu fiye da 500 da suka zo daga kasar Sin da kasashen Afirka sun halarci wannan taro, tare da rattaba hannu kan kwagilolin hadin gwiwa 21, jimillar kudinsu kuma ta kai sama da dala biliyan daya.
Bayan haka, daga ran 3 zuwa ran 5 ga watan Nuwamba na shekarar 2006, an gudanar da taron koli na birnin Beijing, da taron ministoci a karo na 3 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Shugaban kasar Sin Hu Jintao da shugabanni da wakilai daga kasashen Afirka 48, ciki da akwai firaminista Meles Zenawi na Habasha, kasar dake jagoranci wannan taro tare da Sin, sun halarci zaman taron, inda aka zartas da "Shirin birnin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2009", da sanarwar taron koli na birnin Beijing na dandalin tattaunawa.
Bayan haka, daga ran 8 zuwa ran 9 ga watan Nuwamba na bana, za a gudanar da taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a birnin Sharm El Sheikh na Masar, inda Sin za ta yi kokarin kyautata da kuma kara abubuwan dake cikin matakai 8 da ta dauka a wani babban taro na birnin Beijing, a yunkurin ba da tabbaci ga ayyukan hadin gwiwa, da tabbatar da matakan da firaministan Sin Wen Jiabao ya sanar a taron koli kan shirin raya kasa cikin sabon karni na MDD a watan Satumba na shekarar 2008. A sa'i daya, Sin za ta kara wasu matakai a fannin tattalin arziki da cinikayya. Sin za ta ci gaba da karfafa mu'amala da kasashen Afirka da sa kaimi ga samun bunkasuwar dandalin tattaunawa, a yunkurin samar da alheri ga jama'ar Sin da Afirka.
To, jama'a masu sauraro, yanzu bayani ke nan kan tambayar malam Hamissou Abdou, daga katsina, tarayyar Nijeriya, da fatan ka ji kuma ka gamsu da shi. Muna kyautata zaton cewa, Sin za ta ci gaba da karfafa mu'amala da kasashen Afirka, da sa kaimi ga samun bunkasuwar dandalin tattaunawa, a yunkurin samar da alheri ga jama'ar Sin da Afirka baki daya. Game da taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, mene ne ra'ayinku? ko kuna so ku bayyana mana ra'ayinku? Muna maraba da sakwanninku duka, da fatan taron zai sami babbar nasara, idan Allah ya sa. Ni Fatima ke cewa da alheri daga nan sashen Hausa na CRI.(Fatima)