Dakin tseren kekuna na Laoshan

A yammacin birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda za a yi taron wasannin Olympic a shekara mai zuwa, akwai wani dakin tseren kekuna mai suna Laoshan, inda 'yan wasan tseren kekuna za su yi karawa da juna domin samun lambar zinariya a cikin kananan gasannin tseren kekuna guda 12 a shekarar gobe.

Fadin dakin tseren kekuna na Laoshan ya kai kadada misalin 6.6. Tsawon hanyoyin tseren kekuna ya kai mita 200. 'Yan kallo dubu 6 suna iya kallon gasa tare a cikin wannan dakin wasa. Abu mafi jawo hankulan mutane a fannin zayyanar wannan dakin wasa shi ne siffarsa ta yi kama da wata tasa. Masu zayyanar dakin wasan sun zayyana wannan dakin tseren kekuna bisa tsarin yanayin kasa na wurin da aka gina shi yadda ya kamata, ta haka muhimmin bangaren dakin wasan mai siffar tasa ya yi kama da wata hular kwano da 'yan wasan tseren kekuna kan sa a kawunansu a cikin gasa. Duk dakin tseren kekuna na Laoshan ya nuna sigar musamman ta wasan tseren kekuna, wato 'yan wasan tseren kekuna na rubanya kokarinsu domin kara samun sauri a duk ransu.(music)

Sigar musamman ta dakin tseren kekuna na Laoshan mafi janyo hankulan mutane ita ce an yi amfani da yawan sabbin kayayyaki na zamani wajen gina shi, musamman ma samar da haske a cikin dakin wasan. Ana amfani da hasken rana don sassauta dogara da wutar lantarki, ta haka an cimma makasudin kiyaye muhalli da yin tsimin makamashi. Ga misali, a kan rufin dakin wasan, an ajiye babbar tagar gilas. A karkashin wannan tagar gilas kuwa, an yi amfani da allon tattara hasken rana na zamani. In ana rana, ana shigar da hasken rana yadda ya kamata bayan da aka kyautata sassan allon tattara hasken rana. In ana ruwan sama, ana iya shigar da dimbin hasken rana bayan da aka bude wannan allon tattara hasken rana duka. In dare ya yi duhu, saboda an shafa abubuwan musamman a wani bangaren allon tattara hasken rana, in an juya wannan bangare zuwa cikin dakin wasan, irin abubuwan musamman na iya karfafa hasken fitilun da ke cikin dakin wasan. Sa'an nan kuma, irin abubuwan musamman na iya kyautata hasken fitilu yadda ya kamata, ta haka, 'yan wasa za su kara mai da hankulansu kan gasa.

An fara gina dakin tseren kekuna na Laoshan a ran 13 ga watan Oktoba na shekarar 2004 a hukunce, wannan ne sabon dakin wasa na huhu da Beijing ta soma gina domin taron wasannin Olympic na shekarar 2008. Bisa shirin da aka tsara, an kammala gina shi a watan Yuni a shekarar da muke ciki.

Bayanin ba da jagoranci cikin harsunan Sinanci da Turanci


Adireshi da Tel

 

Filayen musamman
Beijing 2008
Sin ciki da waje
Yawon shakatawa
Aiko mana wasika
Gasar kacici-kacici
Jadawalin wasanni
sakonka
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040