Mu hadu A Shekarar 2008 -- Gasar kacici-kacici dangane da Wasannin Olympics ta Beijing
Gabatarwa

Kamar yadda kuka sani cewa, za a gudanar da gasar wasannin Olympics na yanayin zafi a karo na 29 tsakanin ran 8 zuwa ran 24 ga watan Agusta na shekara mai kamawa a nan birnin Beijing, hedwatar kasar Sin. Domin samar muku da wata kyakkyawar damar kara samun ilmi da kuma sa hannu cikin harkokin gasar wasannin, yau dai mun sanar da ku cewa, tun daga ran 1 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki har zuwa ran 1 ga watan Mayu na shekara mai zuwa, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya kaddamar da wata gasar ka-cici-ka-cici mai ban sha’awa a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Gasar Kacici-Kacici ta fara, yi wasa tare da samu abin kyauta!!
Watakila za ka sami mako mai kyau!!
Shiga Gasa
Gabatarwar wasanni

Wannan gasar kacici-kacici ta kasu kashi 3, wato “Wasan wasa kwakwalwa na FUWA”, da “Amsa tambayoyi a kan Internet”, da “Wasannin Olympics a cikin zuciyata”.
Bayan ka ci “Wasan wasa kwakwalwa na FUWA”, sai ka iya amsa tambayoyi 8 a kan Internet, duk wanda ya amsa tambayoyi da kuma ya rututa ra’ayoyinsa game da wasannin Olympic na Beiijing zai sami yiyuwar samun kyauta.
Wa’adin gasa:daga ran 1 ga watan Nuwamba na shekarar 2007 zuwa ran 1 ga watan Mayu na shekarar 2008
Abin kyauta:Duk wadanda suka sami lambar yabo ta musamman cikin wannan gasa za su iya samun damar kawo ziyarar gani da ido a nan Beijing a watan Yuni na shekara mai zuwa da kuma shiga sauran bukukuwa masu kayatarwa da abin ya shafa. Da zuciya daya ne muke fatan za ku sami maki mai gamsarwa a cikin wannan gasa kuma wadanda suka shiga wannan gasa za su sami abin kyauta daga CRI
Hattara: Ka rutuba sunanka da sauran bayananka a kasa, haka kuma, za mu iya gaya maka idan ka ci lambar yabo.
Kuma za a buga duk sunayen mutanen da suka ci lambar yabo a shfinmu na Internet na CRI.

Wanda ya shirya gasa:Rediyon kasar Sin
Wanda ya nuna goyon baya:kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing
Wanda ya yi gasa:CRI online