Dakin cin abinci na HONGBINLOU

An gina wannan dakin abinci na Hongbinlou ne a shekarar 1853, wato yau da shekaru 155 da suka gabata a birnin Tianjin lokacin da ake karkashin mulkin Xianfeng na daular Qing a nan kasar Sin. Ya dade yana da suna sosai wajen dafa abincin musulmai. A shekarar 1955, bisa shawarar da marigayi firayin minista Zhou Enlai ya bayar, an shigar da wannan dakin da ke dafa abincin musulmai a nan birnin Beijing. Sabo da haka, ya yi suna sosai domin abincin musulmai na musamman da aka dafa a cikinsa. Wadanda suka kware sosai wajen abinci da masulmai da bangarori daban daban sun yaba wa dakin abinci na Hongbinlou cewa, "dakin dafa abincin musulmai ne da ke matsayin farko a nan Beijing".

Dakin abinci na Hongbinlou yana da fadin murabba'in mita dubu 2, zai iya daukar mutane 660 da su ci abinci a ciki a lokaci guda.

Manyan baki 'yan siyasa da yawa, ciki har da marigayi shugaban kasar Sin Liu Shaoqi da marigayin firayin minista Zhou Enlai da marigayi firayin minista Edward Richard George Heath na kasar Britaniya da tsohon shugaban kasar Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei da tsohon shugaban kasar Indonesiya Wahid da tsohon firayin ministan kasar Malasiya Datuk Seri Mahathir Bin Mohamad da manyan bakin da suka zo daga kasashen Morocco da Pakistan da Tazania da Tunisiya da Belgium da Italiya da Norway da Khazakstan da Kuwait da Jordan da Iraki sun taba cin abinci a dakin abinci na Hongbinlou.

Bayanin ba da jagoranci cikin harsunan Sinanci da Turanci


Adireshi da Tel

Adireshi: No.11, titin Zhanlanguan, gundumar Xicheng, Beijing

Tel: 8610?68994560, 68992569

Website: http://www.hongbinlou.com.cn

Filayen musamman
Beijing 2008
Sin ciki da waje
Yawon shakatawa
Aiko mana wasika
Gasar kacici-kacici
Jadawalin wasanni
sakonka
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040