Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-24 14:57:09    
"Jiaozi"??takardar kudin da aka fara amfani da ita a duniya

cri

To, shi ke nan, da ma wasu kantuna ne ke sayar da takardar kudi ta "Jiaozi", amma sabo da a kan sami matsala, shi ya sa a shekarar 1023, hukumar daular Song ta arewa ta dau nauyin gudanar da takardun kudin, ta kuma kafa hukumar musamman ta kula da su. Ban da wannan, ta kuma haramta jama'a su fito da takardun kudin da kansu.

Shahararren matafiyi na kasar Italiya, Marco Polo ya taba zuwa kasar Sin, inda ya gano takardun kudi da aka yi amfani da su. A cikin littafin da ya rubuta a shekarar 1298 dangane da tafiye-tafiyensa, ya yi bayani sosai a kan yadda aka bullo da takardun kudi da kuma amfani da su a kasar Sin. Daga littafinsa kuma, Turawa sun fahimci saukin takardun kudi da kuma yadda aka bullo da su.


1 2 3 4 5