A wannan mako, za mu amsa tambayar Bello Abubakar malam Gero, daga tudun Wada Rijiyoyin Dan Umma Bayan Rima Radio, a Jihar Sokoto, tarayyar Nijeriya. Malam Bello ya ce, a wace shekara ce aka soma amfani da kudin takarda a kasar Sin?
Malam Bello da dai sauran masu sauraronmu, a kalla yau da shekaru dubu hudu da suka wuce, aka fara yin amfani da kudade a kasar Sin. Tun farkon fari, an yi amfani da kudin wuri a wajen ciniki, sa'an nan, an kirkiro tsabar kudi da aka yi da karfe ko tagulla ko kuma azurfa, daga bisani, an kuma bullo da takardar kudi, wadda a halin yanzu ta sami karbuwa a duk fadin duniya. To, a game da takardar kudi, kasar Sin ta sha gaban sauran kasashen duniya a wajen fara yin amfani da ita. Yanzu a gyara zama a saurari tarihinta.
1 2 3 4 5
|