Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-23 15:12:42    
Mutanen Baotou na jihar Mongoliya ta gida sun yi iyakacin kokarinsu wajen kare wurare masu damshi

cri

Gwamnatin birnin Baotou ta dora muhimmanci kan wannan yanki mai daraja da take da shi a wurare masu damshi saboda bangaren da take ciki ya kan kamu da dan fari. Shugaban sashen kula da yankuna na kwamitin raya kasa da kawo sauyi na gwamnatin birnin Baotou Mr Wang Xiaoping ya yi farin ciki da bayyana wa wakilin gidan rediyonmu makomar wurare masu damshi dab da rawayan kogi cewa " a halin yanzu da akwai kimanin nau'o'I 37 na tsuntsayen da ke zama cikin ruwa a wurare masu damshi, daga cikinsu da akwai wasu masu daraja sosai da ba a iya ganinsu a birane ba kamar wani babban tsuntsu mai dogon wuya da jar hula. Da aka shiga yanayin kaka,tsire-tsiren da ke akwai a wurare masu damshi sun yi rawaya,sai ka ce wani zane mai ban sha'awa da kyaun gani yana gabankasa lalle kana jin dadin zama a wannan wuri. Da aka shiga yanayin hunturu,dusar kankara na fadowa kasa,sai ka ce wani mayani mai launin fari ya rufe doron kasa,sai ka ce muna cikin wani wuri mai tsabta sosai,hankalinka ya kwanta ba motsi ba kara sai ka ji numfashin kanka kawai kamar kana zamaa wata duniya dabam."

A halin yanzu a wurare masu damshi dab da rawayan kogi,bishiyoyi da ciyayi masu tsanwa shur sun kama furani msu launi iri iri sun tohu,rairayin dake bakin kogi na walkiya kamar hasken zinariya,sai ka ce wani sabon shafi na wurare masu damshi a bude suke,ana jiran mutane su rubuta sabbin kalamomi. Mazauna da yawa na birnin Baotou suna cike da imani kan kyakkyawar makomar wuraren masu damshi na rawayan kogi.


1 2 3 4 5