Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-23 15:12:42    
Mutanen Baotou na jihar Mongoliya ta gida sun yi iyakacin kokarinsu wajen kare wurare masu damshi

cri

Ana nan ana tabbatar da shirin kiyaye wurare masu damshi na dab da rawayn kogi a kai a kai. Da ya ke an fara aikin tabbatar da shirin kare wurare masu damshi,an samun kwarya kwaryar sakamako.darekatan cibiyar kula da wurare masu damshi ta birnin Baotou Mr Yang Yongmin ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa yawan tsuntsaye da na'o'insu da aka samu a yanayin bazara na shekarar nan sun fi na shekarun baya yawa a wurare masu damshi na dab da rawayan kogi.

"Ga shi a yanzu dabbobi da tsuntsaye da ke ciki wurare masudamshi sun karu da sauri,a yanayin bazara na wannan shekara da muke ciki tsuntsaye masu yawon dogon zango sun yada zango a wurarenmu masu damshi,tsuntsayen da ake kira Swan a turance sun yado zango a wurinmu,idan an kwatanta yawansu da na shekarun baya lalle yawansu na karuwa a bayyane,haka kuma sauran na'o'in tsuntsaye su ma suna karuwa."

A tsakiyar watan Afril na wannan shekara, bisa amincewar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da gwamnatin jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta, gwamnatin birnin Baotou za ta shimfida wani filin musamman na kiyaye muhalli na jihar da na kasa baki daya a wurare mau damshi dab da rawayan kogi,tsawonsa ya kai kilomita 220 da fadinsa ya kai kilomita hudu,za a kuma kayatar da wasu wuraren da ke cikin wannan fili domin masu yawon shakatawa. A mai da filin nan zirin karya ga rawayan kogi. Zai iya zama wata hanyar mota ta ba da agaji in ambaliyar ruwa ta faru,haka kuma zai zama wata hanyar yawon shakatawa da ta hada wasu wurare masu kyaun gani sa'ad da masu yawon sha iska ke yawon shan iska.A cikin wuraren da aka kabe domin kare hallita ana iya samun shaidun da suka tabbatar da wayin kai na kabilar Han wajen aikin gona da wayin kai na kabiliyar kanana kabilu wajen kiwon dabbobi,inda kuma aka bayyana ci gaban masana'antun da aka samu a wannan yanki da jihar Mongoliya ta gida.


1 2 3 4 5