Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-23 15:12:42    
Mutanen Baotou na jihar Mongoliya ta gida sun yi iyakacin kokarinsu wajen kare wurare masu damshi

cri

Karar da kuka ji karar wata babbar mota ce da ke dauke da kaya,tana nan tana daukar kayayyakin da aka samu bayan da aka rushe wasu gine ginen da aka kafa ba bisa doka ba. Wannan ya alamanta cewa gwamnatin birnin Baotou ta fara tabbatar da shirinta na kiyaye wurare masu damshi.Madam Wang Xiulian,mataimakiyar shugaban unguwar Jiuyuan ta birnin Baotou ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa kamata ya yi a rushe dukkan gine ginen da aka shimfidu ba bisa doka ba wajen tabbatar da shirin kiyaye wurare masu damshi dab da rawayan kogin.

"Mun dauki wannan mataki ne duk domin rushe daukacin gine ginen da aka kafa ba bisa doka ba a wurare masu damshi."

Wurin da rawayan kogi ta ratsa a yankin birnin Baotou ya sha banbam da na sauran wurare,tsawonsa ya kai kilomita 220 daga gabas zuwa yamma,kogin ya ratsa unguwoyi da dama na birnin, shi ya sa kamata ya yi a tsara wani cikakken shirin kiyaye wurare masu damshi,wannan ba aiki mai sauki ba ne ga gwamnatin birnin Baotou,shugaban sashen kula da yankuna na kwamitin raya kasa da kawo sauyi na gwamnatin birnin Baotou Mr Wang Xiaoping ya bayyana cewa,

"Da farko gwamnatin birnin ta gabatar da wani cikakken shiri,sannan ma'aikatun gwamanatin sun aiwatar da shiri cikin tsanaki,ta haka kuwa kome na tafiya daidai yadda ya kamata mu yi amfani da kowane incin kasa bisa shirin da kuma gina filaye masu kayatarwa."


1 2 3 4 5