Tun tuni, wato a shekarar 1998, kasar Afirka ta kudu ta bayar da sabon shirin tsaron kai. Bisa wannan shiri, kasar Afirka ta kudu ta tsai da kudurin kara saurin zamanintar da na'urorin rundunar soja. A lokacin da take kara karfin yin nazarin sabbin fasahohi da kanta, a karo na farko ne ta aiwatar da shirin sayen makaman zamani daga kasashen waje.
Lokacin da ake cikin zaman lafiya, nauyin da ke bisa wuyan rundunar sojan ruwa ta Afirka ta kudu shi ne, halartar wasu ayyukan diplomasiyya, ciki har da kai wa sauran kasashen duniya ziyara, da yin rangadi da kiyaye jiragen ruwa na kamun kifi a yankunan teku da ke cikin hannun kasar Afirka ta kudu da halartar ayyukan ceto da ba da agaji da yin yaki da laifin fasakwauri da 'yan fashin teku da wadanda ke cinikin makamai ba bisa doka ba.
Bugu da kari kuma, bisa ka'idojin da aka tsara a cikin "dokar harkokin teku ta M.D.D.", rundunar sojan ruwa ta kasar Afirka ta kudu tana rangadi a kudancin yankunan tekun Atlantic da na Indiya. (Sanusi Chen) 1 2 3 4
|