Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 15:01:09    
Kasar Afirka ta kudu ta kara saurin zamanintar da ayyukan sojinta na ruwa

cri

A ran 16 ga watan Oktoba da yamma, wani jirgin ruwan soja kirar Sipioenkop na kasar Afirka ta kudu ya isa wata tashar jirgin ruwa da ke cikin kogin Yangtse a birnin Shanghai na kasar Sin kuma ya soma yin ziyara ta kwanaki biyar a nan kasar Sin bisa gayyatar da rundunar sojan ruwa ta kasar Sin ta yi masa domin taya murnar cika shekaru 10 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu. Wannan ne karo na farko da wani jirgin ruwan soja na kasashen Afirka ya kawo wa kasar Sin ziyara.

Kafin wannan jirgin ruwan soja na kasar Afirka ta kudu ya tashi daga kasar Afirka ta kudu, Mr. Christopher Manick, kyaftin din wannan jirgin ruwa ya gaya wa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, sojojin ruwa na kasar Afirka ta kudu suna jin alfahari sosai domin kawo wa kasar Sin ziyara a karo na farko. Suna fatan za su iya yin koyi da juna da yin musanye a tsakaninsu da sojojin ruwa na kasar Sin.


1 2 3 4