Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 15:01:09    
Kasar Afirka ta kudu ta kara saurin zamanintar da ayyukan sojinta na ruwa

cri

Mr. Manick ya ce, bayan da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen Afirka ta kudu da Sin a shekarar 1998, ana yin cudanya da hadin guiwa cikin hali mai kyau a tsakanin sojojin kasashen biyu. A watan Disamba na shekara ta 2001, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan "takardar fahimtar juna irin ta sada zumunta a tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Jama'ar Sin da gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta kudu", an kuma kafa wani kwamitin tsaron kai na kasashen Afirka ta kudu da Sin. Ya zuwa yanzu wannan kwamitin tsaron kai da ya shirya taruruka ukku ya riga ya zama wani muhimmin dandalin raya da kuma karfafa tabbataccen hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta kudu kan harkokin soja da tsaron kai.

A cikin alfahari ne, Mr. Manick ya ce, a lokacin yakin duniya na biyu, sojojin ruwa na kasar Afirka ta kudu sun taba shiga yaki da sojoijn Jamus. A yankin kudancin tekun Atlantic sun yi yaki da sojin Jamus da ke karkashin ruwan teku, kuma sun sha nasara kwarai.


1 2 3 4