Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 15:01:09    
Kasar Afirka ta kudu ta kara saurin zamanintar da ayyukan sojinta na ruwa

cri

A cikin dakin nune-nunen tarihin sojin ruwa na Afirka ta kudu da ke garin Simon, inda hedkwatar sojin ruwa ta Afirka ta kudu take, Mr. Beckman Tulin ya bayyana yadda kasar Afirka ta kudu take zamanintar da rundunar sojan ruwa ta kasar. Ya ce, ba ma kawai kasar Afirka ta kudu tana shigar da makamai da sauran kayayyakin zamani daga kasashen waje ba, har ma tana nazarin kayayyakin soja da kanta domin kara saurin zamanintar da rundunar sojan kasar. Kasar Afirka ta kudu ta taba sayen jiragen ruwa na zamani daga kasashen Faransa da Ingila da Jamus.

Mr. Tulin ya ce, lokacin da rundunar sojan kasar Afirka ta kudu take kashe makudan kudade domin sayen kayayyakin soja na zamani daga kasashen waje, tana kuma mai da hankali kan ayyukan nazari da kirkiro sabbin kayayyakin soja na zamani. Yanzu karfin nazarin kayayyakin soja na kasar Afirka ta kudu ya samu kyautatuwa. Tsarin harba makamai masu linzami na daga kasa zuwa sama kai tsaye kirar "Mashi" da kasar Afirka ta kudu ta yi nazari, kuma ta kera shi da kanta yana matsayin gaban sauran kasashen duniya.


1 2 3 4