Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 15:21:21    
Wata kwararriyar 'yar wasa ta lankwashe jiki a wasannin Olympics na Beijing

cri

Chusovitina ta fi kwarewa a wasan hawan dokin karfe. A cikin shekarun baya,sau takwas ta samu lambobin zinariya a gasar duniya a wannan fanni. Duk da haka wata 'yar wasa Chen Fit a kasar Sin ta fito a fili, ta canza yanayin da ake ciki a wannan wasan hawan dokin karfe. A wasannin Olympics da ake yi a birnin Beijing ana iya gana takara da ake yi tsakaninsu,da ya ke su abokan gaba ne na juna a filin gasa,Chusovitina ta nuna kaunarta ga wannan 'yar wasa ta kasar Sin.ta ce,

"ina girmamawa da kauna wannan yarinya ta kasar Sin matuka,ina fatan ta samu lambar zinariya a wasan hawan dokin karfe. Gasa gas ace.sakamakon karshe ya bayyana kome. Ina mika fatan alheri zuwa gare ta da ta sami nasara, idan ta kai matsayi na farko a wasan hawan dokin karfe,zan yi farin ciki kwarai da gasket."

Samun lambar zinariya ba abu ne mafi muhimmancin da ake tsammani ga Chusovitina ba,bayyanuwarta a filin takara ta isa abin mamaki a tarihin wasan lankwashe jiki. Kullum ana daukar wasan lankwashe jiki na mata,wasa ne 'yan mata kanana,'yan wasa mata da yawa da suka samu lambobin zinariya da shekarunsu ya kais ha shida ko sha tara,bayan da shekarunsu sun wuce ashirin su kan yi ritaya.amma Chusovitina tana da shekaru sama da talatin da haihuwa tana shiga takarorin duniya tana neman samun lambari zinariya,sai ka ce har wa yau dai tana da kuruciya. Daga baya Chusovitina ta bayyana cewa,

'a ganina abun mafi muhimmanci shi ne kana kishin wannan wasa,idan kana kishin wannan wasa,sai ka niyyata ka ci gaba da kokarinka ka yi kokarin yin wasa,za ka iya ci gaba da aikinka ba tsayawa.'(Ali)


1 2 3 4