Kasar Jamus ta fi ci gaba wajen likitanci,wannan yana da amfani sosai wajen warkar da dana. A sa'I daya kuma Oksana ta samu karin damar shiga gasoshin duniya na wasannin lankwashe jiki a makwafin kasar Jamus,ta kuma samu Karin kudi ta haka ta iya biyan makudan kudaden da ake bukata wajen warkar dad anta. Daga bisani Oksana Chusovitina da iyalinta sun tsungunar da kansu a kasar Jamus,ta kuma wakilci kungiyar kasar Jamus ta shiga takarorin duniya.
Tare da sauri Oksana Chusovitina ta saba da zaman yau da kullum na kungiyar wasan lankwashe jiki ta kasar Jamus, ta fara zama da samu horo da 'yan wasa masu karancin shekaru na kasar Jamus,da yake akwai banbanci tsakaninsu wajen shekaru da harshe kuma al'adu,amma babu Katanga tsakaninsu wajen mu'amala.malamin koyarwa na kungiyar lankwashe jiki ta kasar Jamus William ya ce,
"Da akwai babban aminci tsakanin Oksana Chusovitina da 'yan wasa na kungiyar Jamus.Da ya ke ta fi tsufa cikin kungiyar,ko kusan ba ta yi kamar "mama" ba, ita abokiya ce tasu."
Da ya ke Oksana Chusovitina ta yi ban kwana da kasar Uzbekistan ta shiga rigar 'yar kasa ta Jamus. Mutanen kasar Uzbekistan ba su manta da ita ba,a ganinsu har wa yau dai sun dauki ta abin alfahari ga kasar Uzbekistan. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Uzbekistan Kulbanov ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa,
"Chusovitina,alfahari ne na kasar Uzbekistan.ta ba da babban taimakonta wajen bunkasa wasan lankwashe jiki na kasar Uzbekistan. Mun farin ciki da ganin har wa yau dai tana filin takara na wasan lankwashe jiki, tana da shekaru 33 da haihuwa,sau biyar ta shiga gasa a wasannin Olympics.wannan matsayin koli da ta kago a cikin tarihin Desney. Idan an kwatanta da 'yan wasa mata dake yin wasa tare da ita,suna iya zama 'ya'yanta."
1 2 3 4
|