Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 15:21:21    
Wata kwararriyar 'yar wasa ta lankwashe jiki a wasannin Olympics na Beijing

cri

An haifi Oksana Chusiovitina a kasr Uzbekistan.ta fara shiga takarorin duniya a makwafin tarayyar Soviet kafin shekaru 20 da suka shige. A shekara ta 1992 ne ta shiga wasannin Olympics na duniya,a wannan lokaci ita ce 'yar wasan lankwashe jiki ta tarayya mai cin gashin kanta,ta sami lambar zinari ta kungiya da sauran 'yan wasa a wasannin Olympics da aka yi a Barcelona na kasar Spain.Daga baya a shekara ta 1996,da ta 2000 da ta 2004 ta shiga wasannin Olympics a makwafin kasar Uzbekistan. A cikin shekaru sama da goma da suka wuce,abokanta da 'yan takararta sun yi ritaya daya bayan daya,amma har wa yau dai Oksana Chusovitina tana kan filin wasan lankwashe jiki tare da azama. Da ta waiwayo wasannin Olympics da ba ta iya mantar da sub a, OksanaChusovitina ta bayyana cewa,

"wani karo na wasannin Olympics da ban iya manta da shi ba har abada,shi ne wasannin Olympics na Athen,dalili kuwa shi ne na yi hassara a wannan karo. Ban gwada kwarewata yadda ya kamata ba. Ina fatan Allah ya kare ni in gwada kwarewata ta matsayin kol a nan birnin Beijing.

A hakika bayan da ta samulambar tagulla a gasar duniya ta shekara ta 2002,Oksana Chusovitina ta yi shirin ritaya, amma wata masifa ta zo mata ba zata.shi ya sa Oksana Chusovitina tana ci gaba da aikinta a filin wasan lankwashe jiki.

" A shekara ta 2002,dana ya kamu da cuta,yana fama da sankarar jinin da ake gado. Na zo kasar Jamus ne domin dana ya samu magani a wannan kasa.hadaddiyar kungiyar wasan lankwashe jiki ta kasar Jamus ta ba ni babban taimako. Daga bisani bisa shawarar da ta kawo mini,in sami rigar 'yar kasar Jamus."


1 2 3 4