Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 15:21:21    
Wata kwararriyar 'yar wasa ta lankwashe jiki a wasannin Olympics na Beijing

cri

A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya ruwaito mana kan wata kwararriyar 'yar wasa ta lankwahe jiki a wasannin Olympics na Beijing. A filin wasan lankwashe jiki na mata da ke a nan birnin Beijing,wakilin gidan rediyonmu ya gana da malama Oksana Chusovitina wadda ta zo daga kasar Jamus, 'yar wasa ce ta wasan lankwashe jiki na mata a wasannin Olympics na birnin Beijing,ita ce ta fi yawan shekaru a wasannin Olympics a wannan fanni,duk da haka ya halarci irin wasan har sau biyar a yanzu.Da yake ta fi tsufa a wasan lankwashe jiki na mata, ta fi kwarewa da kasance cikin hali mai kyau. Tare da nasara ne ta sami damar takara a wasan hawan dokin karfe. Tana da shekaru 33 da haihuwa,amma ta yi kokarin neman samun lambobin girmamawa a wannan wasannin Olympics na Beijing.

"Karo na farko na shiga wasannin Olympics ne da 'yan wasa na kungiyarmu,amma yanzu karo na biyar ne da na shiga wasannin Olympics na duniya tare da 'yan wasanmu.na yi farin ciki da samun damar shiga wasannin Olympics."

Oksana Chusovitina ta yi wannan Magana ne bayan da ta kammala wasan fidar gwani na lankwashe lankwashe na Olympics,ta kuma samu damar shiga gasa ta karshe kan hawan dokin karfe. Oksana Chusovitina da ta halarci wasannin Olympics sau biyar ta yi takara da abokan gabanta 'yan wasa mata da shekarunsu na tsakanin 16 da 17,a hakika tana kan matsayin "mama". Ita ce 'yar wasa daya kawai a duniya da ta shiga wasan lankwashe jiki na mata a wasannin Olympics na duniya har sau biyar.


1 2 3 4