Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-24 15:20:42    
London na kokarin shirya wata gasar wasannin Olympics ta kiyaye muhalli

cri

Ban da wannan kuma Madam Nimmo ta bayyana cewa, a gun gasar wasannin Olympics ta London, za a samar da wutar lantarki bisa karfin iska, kuma za a yi la'akari da samun dauwamammen ci gaba lokacin da ake gina muhimman ayyukan yau da kullum da kuma filaye da dakunan wasannin motsa jini, domin su zama wani kashi na abubuwan tarihi na wasannin Olympics. Haka kuma birnin London zai koyi sakamako mai kyau daga sauran biranen da suka taba daukar nauyin gudanar da wasannin Olympics, musamman ma birnin Beijing da ya shirya gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008. Kuma ya kara da cewa,

"Abokan aikinmu sun yi cudanya tare da kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing sosai, kuma mun samu dimbin sakamako masu kyau. Beijing yana da filaye da dakunan wasannin motas jini na ajin farko a duniya, da kauyen 'yan wasannin Olympics mai ban mamaki, da kuma kyawawan gine-gine, shi ya sa tabbas ne za a yi farin ciki sosai a gun wannan gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi. Abubuwan da za mu tsara ba za su yi daidai da na Beijing ba, amma mun koyi fasahohi da yawa daga wajensa, haka kuma mun zama abokan hadin gwiwa ta aminci."(Kande Gao)


1 2 3 4