Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-24 15:20:42    
London na kokarin shirya wata gasar wasannin Olympics ta kiyaye muhalli

cri

Yanzu an riga an fara gina filaye da dakunan wasannin Olympics na shekara ta 2012 da ke gabashin birnin London. Kamar yadda birnin Beijing ya yi, London yana dukufa kan shirya wata gasar wasannin Olympics ta kiyaye muhallin halittu. Madam Alison Nimmo, wata jami'ar hukumar gudanar da ayyukan wasannin Olympics na London na shekara ta 2012 wadda ta kasance hukumar cibiya mai kula da harkokin gina filaye da dakunan wasannin motsa jiki ta bayyana cewa,

"Ko Shakka babu, wasannin Olympics na yanzu ya sha bamban sosai da na shekara ta 1908 da kuma na shekara ta 1948. A wancan lokaci, kwamitin wasannin Olympics na duniya shi ne ya same mu kai tsaye wajen shirya gasar a maimakon mu kanmu mun nemi samun iznin shirya gasar. Haka kuma wasannin Olympics na wancan lokaci ba gagarumai ba ne, muhimman kayayyakin da muka yi amfani da su a gun gasar kayayyakin wasannin motsa jiki ne da muka riga muka mallaka."


1 2 3 4