Madam Nimmo ta bayyana cewa, an fi mai da hankali a kan kiyaye muhalli lokacin da ake gina filaye da dakunan wasannin Olympics na London na shekara ta 2012, a ciki, aikin gina muhimmin dakin wasannin Olympics wanda ake kiransa "babban kwano" zai bi ka'idojin kiyaye muhalli da samun dauwamammen ci gaba. Kuma ta kara da cewa,
"Mun ba da wani babban aiki ga masu zayyane-zayyane, wato ya kamata muhimmin dakin wasannin motsa jiki ya iya daukar mutane dubu 80, amma bayan wasannin Olympics, yawan kujerun da ke cikin dakin zai ragu zuwa dubu 25. Mun girke kujeru dubu 55 da ake iya babbale su tare da fatan yin amfani da su a sauran wurare. Kuma makasudinmu shi ne gina wani dakin da za a ci gaba da yin amfani da shi sosai bayan gasar wasannin Olympics, da kuma samun wuraren da za a yi mafani da wadannan kayayyakin wucin gadi. Yanzu muna yin tuntuba tare da sassan da ke cikin kasar Birtaniya da kuma birnin Chicago na kasar Amurka. Idan za a iya yin amfani da su a cikin wasannin Olympics na gaba, to ya yi kyau kwarai."
1 2 3 4
|