Game da kudurin da jam'iyyar ANC ta neme shi da ya yi murabus daga mukaminsa, Mr. Mbeki bai ji mamaki ba. Sabo da ya kasance da irin wannan alama tun da wuri. Bisa tsarin mulkin kasar Afirka ta kudu, dole ne aka zabi shugaban kasar bisa dan takara da jam'iyyar Babban Taron Jama'a ta Afirka ta kudu ta gabatar, sannan an zartas da shi a gun majalisar dokokin kasar. Jam'iyyar ANC tana yin tasiri sosai ga shugaban kasar Afirka ta kudu. Bayan da Mr. Mbeki ya fadi a cikin zaben shugaban jam'iyyar ANC a shekarar bara, wannan ya almanta cewa, matsayinsa na shugaban kasar ya rasa gindi. Matsaloli iri iri, kamar su matsalar karancin wutar lantarki da matsalar korar mutanen kasashen waje da karfin tuwo da dai makamatansu da suka auku a kasar Afirka ta kudu sun tabbatar da wannan alama. Sabo da Mr. Mbeki bai samu goyon baya daga wajen jam'iyyar ANC ba, matakan daidaita wadannan matsalolin da ya dauka ba su yi aiki kamar yadda ake so ba. Sakamakon haka, jama'ar kasar sun zarge shi sosai. Mr. Mbeki shi kansa ma ya gaji sosai.
Bayan da Mr. Mbeki ya yi murabus daga mukaminsa, majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu tana fuskantar jerin matsaloli. Matsala ta farko ita ce yaya za a zabi wani sabon shugaban kasar domin maye mukamin da Mr. Mbeki ya bari. Amma a takaice dai, za a soma sabon lokaci a kasar Afirka ta kudu bayan Thabo Mbeki. (Sanusi Chen) 1 2 3 4
|