Thabo Mbeki da Jacob Zuma tsoffin abokai da takwarori ne a da. Bayan da Thabo Mbeki ya hau kan mukamin shugaban kasar Afirka ta kudu a shekarar 1999, ya nada Jacob Zuma mataimakinsa. Amma daga baya, huldar da ke tsakaninsu ta karyu a kai a kai. Manazarta suna ganin cewa, bayan da Mr. Mbeki ya kori Mr. Zuma daga mukamin mataimakin shugaban kasar Afirka ta kudu a shekara ta 2005 sabo da an zargi Mr. Zuma da yana da hannu a cikin wata matsalar rashawa da al'amubazzaranci, an soma samun sabane-sabane a cikin jam'iyyar Babban Taron Jama'a ta Afirka ta kudu. Kuma bayan da aka zabi Jacob Zuma da ya zama shugaban jam'iyyar ANC a shekarar da ta gabata, irin wadannan sabane-sabane sun kara yin tsanani.
1 2 3 4
|