Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-22 15:45:10    
Thabo Mbeki ya yi murabus daga mukamin shugaban kasar Afirka ta kudu

cri

A gun wani taron manema labaru da aka yi a ran 20 ga wata, Mr. Gwede Mantashe, babban sakataren jam'iyyar ANC ya bayyana cewa, a gun taron zaunannen kwamitin jam'iyyar, an tsai da kudurin neman Mbeki da ya yi murabus daga mukamin shugaban kasar kafin wa'adinsa na aiki ya kare. Kuma an riga an gabatar da wannan kuduri zuwa ga majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu. Yanzu ana jiran a zartas da shi a gun taron majalisar. Mr. Mantashe ya ce, bayan da Thabo Mbeki ya samu wannan kuduri, bai ji makaki ba, ya ce ya yi maraba da wannan kuduri, kuma ya yarda da a gabatar da wannan kuduri zuwa ga taron majalisar dokokin kasar. Mr. Mantashe ya jadadda cewa, jam'iyyar ANC ya nemi Thabo Mbeki da ya yi murabus daga mukaminsa ba domin tana son zargin Mbeki ba, an tsai da wannan kuduri ne domin ana kokarin kawar da sabane-sabanen da ke kasancewa a cikin jam'iyyar da kara neman hadin kai a cikin jam'iyyar.

Ya kamata a kare wa'adin aiki na shugaba Thabo Mbeki ne a tsakiyar shekara ta 2009, kuma Mr. Jacob Zuma, shugaban yanzu na jam'iyyar ANC shi ne dan takara mafi karfi wajen neman mukamin shugaban kasar Afirka ta kudu a zabe mai zuwa.


1 2 3 4