A ran 21 ga wata, Mr. Thabo Mbeki, shugaban kasar Afirka ta kudu ya bayar da wani jawabi a gidan talibijin kasar, inda ya sanar da yin murabus daga mukaminsa na shugaban kasar Afirka ta kudu. A cikin jawabinsa, Mr. Mbeki ya ce, shi da gwamnatinsa ba su taba tsoma baki kan harkokin shari'a ba, kuma ba su taba sa hannu kan hukumar bincike ta kasar da ta kai kara ga Jacob Zuma, shugaban yanzu na jam'iyyar Taron Jama'ar Afirka ta kudu, wato ANC da laifin rashawa da al'amubazzaranci. Amma domin tabbatar da hadin kai a cikin jam'iyyar. Ya yanke hukuncin amincewa da kudurin neman shi da ya yi murabus daga mukaminsa na yanzu da jam'iyyar ANC ta yi, kuma ya riga ya gabatar da wasikar neman yin murabus daga mukaminsa ga majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu. Wannan ya almanta cewa, za a kawo karshen lokacin Thabo Mbeki a dakalin siyasa na kasar Afirka ta kudu, kuma za a samu wani sabon shugaba a kasar.
1 2 3 4
|