Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-11 15:11:58    
Labari kan masu sa kai na wasannin Olympics na Beijing

cri

Shi Zhange ya bayyana cewa, " bisa shirin da aka tsara,nauyin da ke bisa wuyata shi ne na yi aiki a fannin binciken 'yan wasan hockey.wato bayan da aka kammala gasa,bisa umurnin da sassan da abin ya shafa suka bayar cikin hadin gwiwa,mun sanar da 'yan wasan da suka shiga gasar wasan hocky da aka tuhume su da sha maganin kara kuzari,sai aka kai su wurin aka yi musu bincike," wasu ma'aikatan dake a ofishin binciken ba su bukatar ilimin sana'a ba,nauyinsu shi ne a sanar da 'yan wasan da abin ya shafa a yi musu jagora da su yarda a yi musu bincike, su yi mu'amala da 'yan wasa yadda ya kamata.idan wadannan ma'aikata ba su iya tafiyar da ayyukansu yadda ake bukata ba,an gaza gudanar da aikin bincike,har ma ya kawo mugun tasiri ga yanayin gudanar da wasannin Olympics na birnin Beijing.A ganin malami Shi Zhange shi gada ne na tsakanin ofishin binciken maganin da 'yan wasan suka sha ba bisa doka ba da 'yan wasan da abin ya shafa. Ya ce, " a ganina ni gada ne tsakanin ofishin binciken maganin da aka shad a 'yan wasan da abin ya shafa.na yi iyakacin kokarina domin tabbata a gudanar da wasannin Olympics bisa adalci kuma a fili.aikina shi ne na tabbatar da umurnin da ofishin binciken magani ya bayar na sanar da 'yan wasan da abin ya shafa. Na kan yi wa 'yan wasan bayani. Su ma su kan yi mini tambaya "me ya sa a yi mini bincike."

Daga cikin ma'aikatan masu sa kai da aka same su a jami'ar koyon ilimin wasanni ta birnin Beijing,tsiraru ne suka yi aiki a sassa masu muhimmanci kamar Shi Zhange ke ciki,yawancinsu suna aiki a sassa nay au da kullum. Li Daqiang, wani saurayi ne mai shekaru 21 da haihuwa tare da alfahari ne ya yi bayani kan aikinsa. Ya ce ya yi aiki a sashen kula da tseren kekuna masu hawa kan tuddai na wasannin Olympics na Beijing, ya yi ayyukan share fage domin tabbatar da tseren kekuna masu hawa yadda ya kamata.


1 2 3 4 5