A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani labarin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya samu kan masu sa kai na wasannin Olympics na birnin Beijing. "murmushin masu sa kai,shi ne suna ne mafi kyau na birnin Beijing", wannan jig one na tunanin masu sa kai na wasannnin Olympics na Beijing na shekara ta 2008. yayin da ake yin wasannin Olympics na yanayin zafi a karo na 29, masu sai kai dubu dari biyar sun nuna kwazo da himma suna bautawa 'yan wasa da ma'aikatan dake aiki a filayen wasannin Olympics tare da murmushi a fuskokinsu,ayyukan taimakon da suka yi sun samu yabo daga mutanen gida da na waje.
Jami'ar koyon wasannin motsa jiki ta birnin Beijing dake arewa maso yammancin birnin, jami'a ce ta koli a kasar Sin a fanning wasannin motsa jiki. Tana daukar nauyin binciken ilimin kimiyya na wasannin Olympics kuma tana daukar 'yan wasa ta ba su horo yadda za su iya shiga gasa,har ma ta sama da mutane masu sa kai masu yawa ga wasannin Olympics.Bisa kididdiga da aka yi,an ce masu sa kai da wannan jami'a ta dauka sun kai sama da 3500. Shi Zhange,wani dalibi ne na aji na uku a fanning koyon ilimi na game da jikin mutum na jami'ar nan kullum yana kishin wasannin motsa jiki, da ya samu labarin daukar ma'aikata masu sa kai domin wasannin Olympics na Beijing,sai nan da nan ba tare da bata lokaci ba ya yi rajista.ya ce da akwai dalilai guda biyu da suka sa yana so ya zama dan sa kai na wasannin Olympics na Beijing.Ya ce, 1 " wasannin Olympics na birnin Beijing,wasanni ne mafi kasaita ga mutanen duniya baki daya. A kan matsayin masu kishin wasanni, ina so in shiga aikin sa kai,in samu damar ganin yadda aka gudanar da wasanni cikin fara'a da hadin gwiwa da kuma jituwa,na biyu ina so in ba da taimakona ga kasa ta yadda mutane na sauran kasashen duniya su kara fahimtarsu kan kasar Sin. Bayan da aka yi masa jarrabawa ta rubutu da hira,burinsa ya cika ya zama wani ma'aikaci a ofishin binciken maganin sa kuzarin da 'yan wasa suka sha ba bisa doka ba. Wannan aiki ya sha banban da na saura,ya kamata mai aiki yana da ilimi na musamman a wannan fanni.
1 2 3 4 5
|