Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 22:35:36    
An rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a nan birnin Beijing

cri

Bala: Masu sauraro, shirin da kuke saurara shi ne shirin musamman na bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Lubabatu: Yau da shekaru 7 da suka gabata, a cikin rahoton kimantawa kan birnin Beijing da kwamitin wasannin Olympics na duniya ya bayar, an bayyana cewa, ta hanyar shirya wata gasar wasannin Olympics a birnin Beijing, za a bar abubuwan tarihi na musamman ga kasar Sin da wasannin motsa jiki na duniya. Kuma a yau, wato lokacin da ake bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing, bisa hakikanan abubuwan da ya yi, Beijing ya shaida cewa, lalle kasar Sin da duniya da kuma wasannin Olympics dukkansu sun samu alheri daga wajen gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Bala: "Bayan da aka kammala wasannin Olympics na Beijing, za a ci gaba da yin amfani da kayayyakin Olympics masu inganci domin jin dadin jama'a. Hasken zuci da Sinawa ke nunawa a wasannin motsa jiki da kuma wasannin Olympics zai ci gaba da karuwa. Na yi imanin cewa, za a kara samun ingantatuwar ruhun wasannin motsa jiki a kasar Sin domin kai shi wani sabon matsayi."

Lubabatu: To, masu sauraro, abin da kuke saurara dazun nan fahimta ce da Colin Moynihan, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Birtaniya ya yi kan tasirin da gasar wasannin Olympics ta Beijing zai bai wa kasar Sin. Haka kuma Mr. Heiberg, shugaban sashen raya kasuwanni na kwamitin wasannin Olympics na duniya ya bayyana ra'ayinsa kan batun, cewar,

Bala: "Bayan wasannin Olympics, kasar Sin za ta jawo hankulan dimbin mutane masu yawon shakatawa, kuma tattalin arziki da masana'antu na kasar za su samu bunkasuwa sosai. In an yi hangen nesa, ba birnin Beijing kawai ba, har ma duk kasar Sin za ta ci gajiya daga lamarin."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11