Lubabatu: A waje daya kuma, a lokacin da yake jawabi a gun bikin rufe gasar Olympic ta Beijing, Mr. Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasanin motsa jiki na Olympic na kasa da kasa ya yaba wa sakamakon da aka samu a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing. Mr. Rogge ya ce, "Mun gode wa jama'ar kasar Sin. Mun gode wa dukkan mutane masu aikin sa kai. Mun gode wa kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing. Ta hanyar shirya wannan gasar Olympic, kasashen duniya sun fi sanin kasar Sin, kasar Sin ta fi sanin sauran kasashen duniya. Dukkan 'yan wasa da kuke gasar yau, ku hakikanan abin koyi ne. Kun bayyana karfin hada kan jama'a na wasannin motsa jiki kamar yadda ya kamata. Lokacin da 'yan wasa da suka zo daga kasashen da suke adawa da juna suke rungume da juna, suna bayyana ainihin ruhun Olympic. Ina fatan bayan komawarku a kasashenku, irin wannan ruhu zai ci gaba da kasancewa har abada. Wannan wasannin Olympic ne mai kyau da ba safai a kan ga irinsu ba."
Bala: A gun bikin rufewa, Mr. Guo Jinlong, magajin birnin Beijing ya mika wa shugaba Jacques Rogge na kwamitin wasannin motsa jiki na Olympic na kasa da kasa tutar Olympic mai zobba 5. Sannan Mr. Rogge ya mika wannan tuta zuwa ga hannun Boris Johnson, magajin birnin London, wato mai masaukin gasar wasannin Olympic ta karo na 30 ta shekarar 2012. Wannan ya almanta cewa, birnin London ya karbi sandar shirya gasar wasannin Olympic a hukunce.
Lubabatu: A karkashin idanun dubban jama'a, sannu a hankali ne aka kashe wutar wasannin Olympic da ta ci har na tsawon kwanaki 16. An gama gasar wasannin Olympic cikin nasara.
1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
|