Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 22:35:36    
An rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a nan birnin Beijing

cri

Bala: Hale Wendy ita ce daya daga cikin 'yan wasa uku da suka zo daga kasar Tsibiran Solomon. Ta shiga gasar daukan nauyi na ajin kilo 58 na mata, amma ta zama na karshe, duk da haka, ba ta yi bakin ciki ba, ta ce,

Lubabatu: "Na yi alfahari sosai saboda na samu iznin zuwa Beijing, ni ma na yi alfahari saboda na shiga gasar wasannin Olympic, wannan ne karo na farko da na shiga gasar wasannin Olympic, ban da wannan kuma, na yi alfahari saboda ni ce 'yar wasan daukan nauyi daya kadai daga kasarmu."

Bala: Abin da ya fi burge jama'a shi ne, wasu 'yan wasanni musamman masu kakkarfar niyya sun halarci wasannin Olympics na Beijing.

Lubabatu: A ranar 12 ga wata, a lokacin da 'dan wasan iyo na kasar Amurka Eric Shanteau, wanda ya samu ciwon sankara, ya shiga cibiyar wasan iyo ta kasar Sin da ke birnin Beijing, da ake kira 'water cube' mai siffar 'tafkin wanka', dimbin 'yan kallon wasa sun yi sowar farin ciki don yin lale marhabin da shi.

Bala: A ranar 13 ga wata da yamma, a gun gasar share fagen wasan kwallon tebur da aka shirya a zagaye na farko tsakanin kungiyar 'yan wasa mata, akwai wata 'yar wasa da ta rasa damtse na dama daga kungiyar wasanni ta kasar Poland, ita ce Natalia Partyka, wadda ta taba samun lambar zinariya a gun gasar kwallon tebur ta tsakanin mace da mace a gun wasannin Olympics na nakasassu na Athens. Ban da wannan kuma, wata 'yar wasa daga kasar Afirka ta kudu Natalie Du Toit, wadda ta rasa tafin kafa na hagu, ita ma ta halarci gasar iyo. Partyka ta ce, tana fatan za su karfafa imanin nakasassu.

Lubabatu: "Idan ayyukana na iya bayar da kwarin gwiwa ga nakasassu da yawa da su shiga wasannin motsa jiki, to wannan zai zama wani abu mai kyau. Ina fatan labarun da aka bayar game da ni da wancan 'yar wasa ta kasar Afirka ta kudu za su kara imani ga abokanmu nakasassu, wato idan ka yi iyakacin kokari, kuma ka hakkake kanka, to, za ka cimma burinka."

Bala: Masu sauraro, kuna nan sauraren shirin musamman da sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin ke gabatar muku game da bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Lubabatu: A lokacin da 'yan wasan motsa jiki suke yin kokarinsu, a waje daya kuma, an tabbatar da babban makasudin da kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya gabatar na "shirya wasannin Olympics mai sigar musamman, kuma bisa babban matsayi", bayan haka kuma, an tabbatar da tunani a fannoni uku , wato "wasannin Olympics da ke da muhalli mai kyau, da fasahar zamani, da kuma al'adu nagari."

Bala: "Ko shakka babu, an gudanar da wasanni kamar yadda ya kamata. Mun ga dakuna da filayen wasannin motsa jiki masu kyau, da gasannin fid da gwani. Amma, abin da ya fi muhimmanci shi ne, an shirya wasannin lami lafiya. Kazalika kuma, an daidaita dangantakar da ke tsakanin jami'an kasashe da na duniya kamar yadda ya kamata. Ya zuwa yanzu, mun gamsu da kome da kome."

Lubabatu: Wannan ne yabo da daraktan zartaswa na wasannin Olympics na hukumar wasannin Olympics ta duniya Gilbert Felli ya nuna wa wasannin Olympics na Beijing.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11