Lubabatu: A yayin da birnin Beijing yake neman izinin shirya gasar wasannin Olympics, ya gabatar da ra'ayin wasannin Olympics na kimiyya da fasaha, a halin yanzu dai, an riga an cimma burin shirya gasar wasannin Olympics da kimiyya da fasaha. Bari mu ga wani musali, babban filin wasannin Olympics na Beijing da ake kira "shekar tsuntsu" ya karya matsayin bajimta da yawa, wanda ya fi girma, ya fi yin amfani da bakin karfe, ya fi yin amfani da kimiyya da fasaha na zamani, ya fi tsara tsari mai kyau, ya fi wuyar ginawa. A duk yukunrin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing, an yi amfani da kimiyya da fasaha na zamani daga dukkan fannoni. Game da haka, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin kuma ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wan Gang ya ce,
Bala: "Domin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing da ke da abubuwan musamman da matsayi mai kyau, bangarorin da abin ya shafa na kasar Sin sun tsara manyan ayyuka goma a fannonin kimiyya da fasaha. Bayan da aka yi amfani da su a gun gasar wasannin Olympics, za su iya taka rawa a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma."
1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
|