A lokacin da take waiwayo haka, Guo Wenjuna ta ce,
"Na sha wahala sosai a yunkurin samun horo, lallai na yi godiya sosai ga taimakon da mutane da yawa suka ba ni, ta yadda na ke iya samun damar nuna, da kuma shaida kwarewata a gasar."
A shekarar da ta janye jiki daga kungiyarsu, Guo Wenjun ta bar gidanta, kuma ta sayar da tuffafin motsa jiki a wani kanti, a lokacin ta sha wahalar zaman rayuwa sosai. Saboda haka, a lokacin da ta sake komawa gasar wasan harbe-harbe, ta san wane abu ne da take so. Tare da juyewar ra'ayi kuma, ta soma samun sakamako mai kyau a wasanni daban daban. A shekarar 2006, ta shiga kungiyar wasan harbe-harbe ta kasar Sin. A gun wasannin Asiya na Doha da aka shirya a karshen shekarar, Guo Wenjun, wadda a karo na farko ne ta shiga gasar duniya, ta samu lambar azurfa a gasar harbe-harben fisto ta mita 10. Daga baya kuma, sai ta samun lambobin zinariya a jere a gasar cin kofin Asiya, da ta duniya, har ma haddadiyar kungiyar harbe-harbe ta duniya ta zabe ta da ta zama 'yar takarar neman 'yar wasa da ta fi kwarewa a wannan shekara.
1 2 3 4
|