A farkon wasan harbe-harbe, Guo Wenjun ba ta nuna gwaninta sosai kan wannan ba, har ma ta gamu da wahalili da yawa. A wasan birane a karo na biyar na kasar Sin da aka shirya a shekarar 2003, GuoWenjun ba ta samu sakamako mai kyau ba. Bayan haka kuma, a duk shekarar 2004, ba ta samu wata damar shiga wasanni bisa matsayin dukkan kasar ba. A shekarar 2005 kuma, Guo Wenjun ta shiga kungiyar wasan harbe-harbe ta lardin Shanxi ta kasar Sin, amma a karshe dai ba ta halarci wasannin dukkan kasar a karo na 10. A sakamakon haka, Guo Wenjun ta gabatar da rahoton janye jiki daga kungiyarsu, kuma ta yi hutu har fiye da shekara daya. Amma, a karkashin taimakon da mai horar da ita, da iyalanta suka yi mata, Guo Wenjun ta sake kwarin gwiwarta don komo filin horo.
1 2 3 4
|