Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 15:21:16    
Ana fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta zama wani abin da za a sake tunawa a nan gaba

cri

A lokacin da ake yawo da wutar gasar wasannin motsa jiki na Olympic ta Beijing a duk fadin duniya, kasar Tanzania ita ce kasa kadai da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya zaba a nahiyar Afirka wajen yawo da wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing. Jakada Mapuri ya ce, an samu nasarar yawo da wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a kasar Tanzania, wannan yana bayyana zumuncin gargajiya dake kasancewa a tsakanin kasashen Sin da Tanzania, kuma a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Ya ce, "Da farko dai, a madadin sunana da sunan jama'ar kasar Tanzania, na nuna wa kasar Sin godiya domin ta zabi kasar Tanzania da ta zama kasa daya da aka mika wutar gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing. Wannan ne kuma karo na farko da aka mika wutar gasar wasannin Olymppic a nahiyar Afirka. Jama'ar Tanzania suna jin alfahari sosai, musamman bayan da aka samu nasarar yawo da wutar, jama'ar Tanzania suna farin ciki kwarai da gasket, sun yi waka, kuma sun yi raye raye domin wannan yana almanta karfaffen zumuncin da ke kasancewa a tsakanin kasashenmu. Lokacin da 'yan uwanmu na Tanzania suke tabo Magana kan aikin yawo da wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing, sun ce, ya kamata a yi yawo da wutar a Afirka domin kasar Sin aminiya ce ta duk AFirka."

Jama'ar kasar Tanzania suna sha'awar wasannin motsa jiki, za su zura idonsu kan gasar wasannin motsa jiki na Olympic ta Beijing ta hanyoyi iri daban daban. Ba ma kawai suna mai da hankali kan gasar wasannin Olympic ba, har ma sun fi maid a hankali kan al'adun kasar Sin. Mr. Mapuri ya ce, "Jama'ar Tanzania suna fatan za su iya kallon yanayin Beijing da Forbidden City da Babbar Ganuwa da mutum-mutumin soja da na dawaki na farkon sarkin daular Qin, kuma da sauran fannonin da ke bayyana al'adun kasar Sin."

Daga karshe dai, jakada Mapuri yana fatan za a kawo alheri ga gasar wasannin Olympic ta Beijing, ya ce, "Ina fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta samu nasara. Tun bayan isowata a Beijing, na ga ayyukan share fagen gasar da kasar Sin ta yi. Ina cike da imani cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta samu nasara, kuma za ta zama abin da za a tuna da shi a tarihin gasannin wasannin Olympic." (Sanusi Chen)


1 2 3 4