Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 15:21:16    
Ana fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta zama wani abin da za a sake tunawa a nan gaba

cri

Mr. Mapuri ya bayyana cewa, aikin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic yana karfafa huldar da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da na waje, ya kuma sanya jama'ar kasar Sin da su kara bude tunaninsu. Mr. Mapuri ya ce, "Ban da wannan, ina kuma mai da hankali kan huldar da ke tsakanin Sinawa da jama'ar kasashen waje. Yanzu Sinawa suna maraba da 'yan kasashen waje sosai, kuma sun soma koyon harsunan waje. Tabbas ne irin wadannan abubuwa za su amfana wa gasar wasannin Olympic ta Beijing."

A cikin shekaru 2 da suka gabata bayan da ya hau kan mukamin jakadan kasar Tanzania a nan kasar Sin, ba ma kawai Mr. Mapuri yana ta mai da hankali kan aikin share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing a kullun ba, har ma ya kan halarci wasu ayyukan shirya gasar da kansa. "Na kan zura ido kan ayyukan share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing ta hanyar karanta jaridu da kallon shirye-shiryen talibijin da radiyo. Na kuma taba halartar wasu manyan bukukuwa, ciki har da kasaitaccen bikin kidaya sauran kwanaki 100 da gasar wasannin Olympic ta Beijing da aka yi a filin Tian'anmen da ke cibiyar birnin Beijing, kuma na taba halartar bikin maraba da isowar wutar gasar wasannin Olympic a birnin Beijing daga kasar Girka."


1 2 3 4