Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 15:21:16    
Ana fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta zama wani abin da za a sake tunawa a nan gaba

cri

A gabannin gasar wasannin motsa jiki na Olympic ta Beijing, Mr. Ramadhani Omari Mapuri, jakadan kasar Tanzania ya gana da wakilinmu a nan birnin Beijing. Ya bayyana cewa, yana fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta zama wani abin da za a sake tunawa a nan gaba.

Lokacin da ake tabo magana kan kasar Tanzania da ke gabashin nahiyar Afirka, za a iya tunawa da tsaunin Kilimanjaro da mutum-mutumin katako da kabilar Masai da har yanzu suke bin dadadden al'adunsu kuma da namun daji iri daban daban. Haka kuma, kafin ya zama jakadan kasar Tanzania da ke nan kasar Sin, Mr Mapuri shi kuma bai san kasar Sin sosai ba. Mr. Mapuri ya gaya wa wakilinmu cikin harshen Swahili cewa, "Kafin isowata a kasar Sin, akwai wasu alamun da suke cikin zuciyata. Alal misali, na san kasar Sin tana da dadadden tarihi da wadatattun al'adu. Kuma na sani, akwai kekuna masu dimbin yawa a biranen kasar Sin, musamman a nan birnin Beijing. A waje daya kuma, na san kasar Sin tana ta dukufa ka'in da na'in wajen raya tattalin arziki."

Amma bayan da ya zo nan kasar Sin ya zama jakadan kasar Tanzania a nan kasar Sin tun daga shekara ta 2006, abubuwan da Mr. Mapuri ya gani a nan Beijing sun sanya shi da ya san ma'anar "gani ya kore ji". Ya ce, "Abubuwa sun sha bamban sosai da alamun da ke cikin zuciyata, musamman al'adu da tarihi na kasar Sin. Na kai ziyara ga Babbar Ganuwa da Kaburburan Sarkuna guda 13. Haka kuma, kasar Sin ta samu sauye-sauye sosai, musamman yanzu babu kekuna da yawa a birane, akwai motoci masu dimbin yawa da suke gudu a biranen kasar Sin. Bugu da kari kuma, na gano cewa, gine-ginen da aka yi a biranen kasar Sin sun sha bambanci da na da. Yanzu ban iya bambanta kasar Sin da wasu kasashe masu arziki ba."

A idon Mr. Mapuri, irin wadannan sauye-sauye sun kara samun karfafuwa bayan da kasar Sin ta samu izinin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing a ran 13 ga watan Yuli na shekara ta 2001. Ana kuma kara saurin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. Mr. Mapuri ya ce, "A ganina, ana sharen fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing bisa shirin da aka tsara kamar yadda ya kamata. Jama'ar kasar Sin sun yi namijin kokarinsu wajen shirya wannan gasa. Kamar yawancin mutane suke yi, ina kuma mai da hankalina kan ayyukan samar da dakuna da filayen motsa jiki na gasar wasannin Olympic. A waje daya kuma, ina mai da hankali kan ingancin iska. Yanzu ingancin iskar Beijing ya samu kyautatuwa sosai bayan da gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakai wajen tabbatar da ingancin iska, kamar an rufe masana'antu masu gurbata muhalli da aiwatar da sabon ma'aunin fitar da iskar motoci. Haka kuma, na mai da hankali kan yanayin Beijing. Da na sauka daga jirgin sama na iso Beijing, na ga jerin bishiyoyi da yawa da ke kewayen filin jiragen sama da hanyoyin mota da ke hada filin jirgin sama da cikin garin birnin Beijing."


1 2 3 4