Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 15:21:16    
Ana fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta zama wani abin da za a sake tunawa a nan gaba

cri

A gun bikin yada gasar wasannin Olympic ta Beijing da aka yi a ran farko ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya gayyaci John Stephen Akhwari, wani jarumin Olympic na kasar Tanzania. A gun gasar Marathon da aka yi a gasar wasannin Olympic ta birnin Mexico ta shekarar 1968, lokacin da ya ji rauni a kan kafarsa, ya dinka kammala duk gasar. Sabo da haka, wannan matakin da ya yi ya burge dukkan 'yan kallon gasar. Sabo da haka, an ba shi lambar yabo ta jarumin kasar Tanzania. Lokacin da Mr. John Akhwari yake nan kasar Sin, ya samu maraba daga wajen Sinawa. Dangane da haka, game da ma'anar ruhun gasar wasannin Olympic, Mr. Mapuri ya ce, "Ina tsammani Mr. Akhwari yana wakiltar jarumtaka ta ruhun wasannin Olympic. Abin da ya yi a gun gasar wasannin Olympic ta birnin Mexico da aka yi a shekarar 1968 ya gaya mana cewa, halartar gasar wasannin Olympic ba domin lambobin zinariya kawai ba. Idan ba ka samu lambar zinariya, ba a iya fadin cewa ba ka samu kome ba a gun gasar wasannin Olympic. Ko da yake 'yan wasa sun halarci gasar domin neman damar zama zakara, amma wannan ba burin karshe ba ne. Ban da lambar zinariya, za ka iya nuna jarumtaka da karfin hali naka."

Gasar wasannin motsa jiki ta Olympic kasaitacciyar gasa ce ta duk duniya da ta dukkan 'yan Adam. Kirarin gasar wasannin Olympic ta Beijing shi ne "duniya daya, mafarki daya". Wannan kirari yana bayyana ainihin ruhun Olympic, wato hada kai da sada zumunta da neman cigaba da jituwa da halarta da kuma mafarki. Mr. Mapuri ya kuma tabo magana kan "mafarkinsa na Olympic", ya ce, "A gare ni, gasar wasannin Olympic wani mafarki ne. Dukkan kasashen duniya suna hada kan juna sosai a gun gasar wasannin Olympic. A gare ni, mai yiyuwa ne wannan dama kadai da na kalli gasar wasannin Olympic da idona, amma ba kamar a da na kalli gasannin wasannin Olympic a talibiijin ba. Na amince da cewa, ba zan manta da wannan gasar har abada ba."

Ya kasance da huldar gargajiya a tsakanin kasar Sin da kasar Tanzania. Ba ma kawai suna hada kan juna kan harkokin siyasa da na tattalin arziki ba, har ma suna hada kan juna a fannin wasannin motsa jiki. Mr. Mapuri ya ce, "Ana hadin guiwa a tsakanin kasashen Sin da Tanzania a fannoni da yawa, amma har yanzu ya kasance da karin fannoni na yin hadin guiwa a tsakaninsu. Mun riga mun yi hadin guiwa wajen samar da dakuna da filayen motsa jiki, kuma mun taba aika wa juna da 'yan wasanni. A waje daya kuma, kasar Sin ta taba koyar wa yaranmu fasahohin wasan lankwashe jiki. Ina da imani cewa, yanzu lokaci ne na kara yin hadin guiwa a tsakaninmu, musamman a fannonin aika wa juna da 'yan wasannin motsa jiki. Kowa ya sani, wasannin motsa jiki za su iya kara fahimtar juna da zumunci a tsakanin al'ummomi daban daban. Zumuncin da ke kasancewa a tsakanin kasashen Sin da Tanzania yana da dadadden tarihi, zumuncin da ke kasancewa a tsakanin shugabanni da gwamnatoci na kasashen biyu sun kuma zama zumuncin da ke kasancewa a tsakanin jama'ar kasashen biyu. Yanzu yawan Sinawan da suke zuba jari da yawon shakatawa a kasar Tanzania yana ta karuwa. 'Yan kasar Tanzania kuma suna kasuwanci a kasar Sin. Idan mun kara yin hadin guiwa a fannonin wasannin motsa jiki da al'adu, za a kara fahimtar juna a tsakanin jama'ar kasashen biyu."


1 2 3 4