Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 15:51:56    
A shekarar 1980, birnin Moscow hedkwatar tsohuwar tarayyar Soviet ya taba shirya gasar wasannin Olympic ta karo na 22

cri

Babbar matsalar da muka fuskanta ita ce shugaban kasar Amurka Jimmy Carter ya sanar da cewa kungiyar wakilan 'yan wasannin kasar Amurka ba za ta shiga gasar wasannin Olympic ta Moscow ba. Tun daga watan Janairu na shekarar 1980, na kai ziyara a kasashen Amurka da Mexico da dai sauran kasashe don kara yi musu bayani, bai kamata a hada siyasa da gasar wasannin Olympic tare ba. Ta hanyar kokarimmu, wasu kasashe sun tura 'yan wasannin zuwa birnin Moscow, wasu kasashe kamar su Birtaniya da Faransa, ko da yake gwamnati ta kauracewa gasar wasannin Olympic, amma 'yan wasanni sun zo da kansu tsohuwar tarayyar Soviet don halartar wasannin Olympic.

Vitaliy Smirnov yana ganin cewa, a sakamakon kauracewa wasannin Olympic, 'yan wasanni na wasu kasashe ba su shiga cikin gasar wasannin Olympic ba, wannan masifa ce gare su.

Mutanen da suka fi shan wahalhalun kauracewar wasannin Olympic su ne 'yan wasanni, wasu mutane sun ji bakin ciki sosai, sabo da ba su iya samun damar zuwa gasar wasannin Olympic ba. A cikin dukkan rayuwar yawancin 'yan wasanni, suna da dama sau daya ne kawai wajen shiga cikin gasar wasannin Olympic, kalilan ne za su shiga cikin gasar wasannin Olympic sau biyu ko fiye. Sabo da haka, wadannan mutanen da ba su sami damar zuwa gasar wasannin Olympic da aka yi a shekarar 1980 ba su ne mutanen da suka fi shan wahala.


1 2 3 4