Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 15:51:56    
A shekarar 1980, birnin Moscow hedkwatar tsohuwar tarayyar Soviet ya taba shirya gasar wasannin Olympic ta karo na 22

cri

Abun wasannin Olympic mai kawo wa mutane sa'a na Bear mai suna Misha da ke da halayyen musamman na kasar Rasha ya fi burge mu sosai. Kwanakin nan, shugaba mai girmamawa na kwamitin gasar wasannin Olympic na Rasha kuma mataimakin shugaba na farko na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Moscow ta shekarar 1980, Vitaliy Smirnov ya waiwayi aikin wurjaja da suka yi wajen shirya gasar wasannin Olympic na wancan gami. To yanzu bari mu ji labarin da wakilin CRI ya samu daga birnin Moscow.

Vitaliy Smirnov mai shekaru 73 da haihuwa shi ne shugaba mai girmamawa na kwamitin gasar wasannin Olympic na kasar Rasha. Ya taba shirya gasar wasannin Olympic da aka yi a lokacin zafi a shekarar 1980 a birnin Moscow, haka kuma ya taba zama mataimakin shugaba na farko na kwamitin gasar wasannin Olympic na kasar Rasha, kuma ya kula da aikin daidaitawa tsakanin kwamitin gasar wasannin Olympic na duniya da hukumomin motsa jiki na kasashen duniya da kafofin yada labaru. Yayin da ya tabo maganar matsalolin da suka fuskanta yayin da suka shirya gasar wasannin Olympic, Vitality Smirnov ya bayyana cewa, a sakamakon tsohuwar tarayyar Soviet ta girka sojoji a Afganistan a karshen shekarar 1979, kasashen Amurka da sauran kasashe, bi da bi ne suka bayyana cewa, ba za su shiga cikin gasar wasannin Olympic ta Moscow ba, wannan ya kawo babbar matsala ga gasar wasannin Olympic.


1 2 3 4