
A kungiyar wasannin Olympics ta kasar Sin, yawancin zakarun wasannin Olympics, da na duniya sun fito ne daga 'yan wasan da ke karkashin shugabancin Huang Yubin. Huang Yubin yana fatan 'yan wasa na kasar Sin za su samu sakamako mai kyau a gun wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008. Ya ce,
'Ina fatan kungiyar wasannin Olympics ta kasar Sin za ta iya cimma burinsu a gun wasannin Olympics na Beijing, wannan ne kuma fatan alheri da nake nuna wa 'yan wasanmu. Saboda ni kuma wani mai horar da 'yan wasa, don haka na san wahalolin da 'yan wasa, da masu horar da su suka sha."
A karshen ziyarar, Huang Yubin na fatan ta gidan rediyonmu, wato CRI, don yin kira ga mutane mafi yawa da su kula da wasannin Olympics na Beijing:
'Ni ne babban mai horar da 'yan wasa na kungiyar wasan lankwashe jiki ta kasar Sin, ina fatan masu sauraro ku mayar da hankula kan wasannin Olympics na Beijing." 1 2 3 4
|