A kungiyar lankwashe jiki ta kasar Sin, Huang Yubin ya yi suna saboda yana aiki ba sani ba sabo, amma saboda daidai babu sassauci ne, Huang Yubin, da kungiyar lankwashe jiki ta kasar Sin da ke karkashin shugabancinsa sun samun sakamako mai walkiya. Ya zuwa yanzu, 'yan wasa 12 da ke karkashin shugabancinsa sun zama zakarun duniya, sun taba samun lambobin zinariya fiye da 30 a wasu gagaruman wasanni, ciki har da wasannin cin kofin duniya, da wasannin Olympics, da dai sauransu. Bisa sakamako mai kyau da ya samu wajen shugabancin kungiyar, an lakanta wa Huang Yubin suna "Mai horar da 'yan wasan da suka fi samun lambobin zinariya".
Huang Yubin ya gayawa manema labaru cewa, yanzu kungiyar wasan lankwashe jiki ta kasar Sin na shirya sosai don shiga wasannin Olympics, yanzu wahalar da ta fi tsanani a gabanta ita ce, babban matsin lamba da suke fuskanta. Ya ce,
'A ganina, abin da ya fi muhimmanci don sassauta matsin lamba shi ne, fasahar wasan lankwashe jiki."
1 2 3 4
|