Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 15:06:10    
Kai ziyara ga masu yawo da fitilar wasannin Olympic Huang Yubin

cri

A shekarar 1980, Huang Yubin, wanda shekarunsa na haihuwa a lokacin sun kai 22 kawai, ya samu lambar zinariya a gasar rings wato gasar zobe ta wasannin lankwashe jiki na cin kofin duniya, haka kuma ya zama zakarar duniya ta farko a tarihin wasannin lankwashe jiki na maza na kasar Sin. Tun daga lokacin kuma, a matsayinsa na mai horar da 'yan wasanni, Huang Yubin, da kungiyar lankwashe jiki ta kasar Sin da ke karkashin shugabancinsa, suna cigaba da samun lambobin yabo a wasannin duniya. A shekaru fiye da goma da suka wuce, Huang Yubin ya zama wani ainihin 'Mai horar da 'yan wasan da suka fi samun lambobin zinariya' a wasan lankwashe jiki. Saboda haka, aka zabe shi don ya zama mai yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008, wanda ya cancanci a girmama shi. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu yi muku wani bayani game da wannan mai horar da 'yan wasa, wato Huang Yubin, yanzu kuma ga cikakken bayanin.

Halarci bikin yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008, wannan ne karo na uku da Huang Yubin ya zama mai yawo da fitilar wasannin Olympics. A idonsa, bikin yawo da fitilar wani aikin motsa jiki ne da kowa da kowa ke iya halarta. Ya ce,

'Game da wasannin motsa jiki na guje-guje, a fi mayar da hankali kan nuna kwarewa a wasanni. Amma kan wasannin da aka yi a tsakanin jama'a kuma, abin da ya fi muhimmanci shi ne shiga wasanni, ta yadda za a iya gina jiki. A ganina, wasannin motsa jiki na guje-guje, da wasannin da aka yi a tsakanin jama'a su ne 'yan uwa da ba a iya rarrabe su ba, wasannin motsa jiki na guje-guje ya kawo bunkasuwar wasannin jama'a, a waje daya kuma, wasannin jama'a ya ciyar da bunkasuwar wasannin motsa jiki na guje-guje. Na shiga aikin yawo da fitilar bisa matsayina na wani mai horar da 'yan wasa na wasannin motsa jiki na guje-guje, wannan na iya nuna fahimta da kuma sanar da hasashen wasannin Olympics, da wasannin da aka yi a tsakanin jama'a.'


1 2 3 4