Huang Yubin na gudanar da ayyukan lankwashe jiki har na tsawon shekaru fiye da 40. A shekarar 1980, ya samu lambar zinariya ta gasar wasan zobe a wasannin lankwashe jiki na cin kofin duniya. A shekarar 1985, Huang Yububin ya zama mai horar da 'yan wasa na kungiyar wasan lankwashe jiki ta mata ta kasar Sin, kuma ya yi amfani da hanyar horar da kungiyar wasa ta maza kan kungiyar wasa ta mata. Bayan shekaru uku da suka wuce, Fan Di, 'yar wasa da ke karkashin shugabancinsa, kuma shekarunsa na haihuwa ya kai 14 kawai a lokacin, ta zama zakara da maki goma, wato cikakken maki a gasar cin kofin duniya ta lankwashe jiki a karo na 24. A shekarar 1988, matsayin kwarewa na kungiyar wasan lankwashe ta maza ta kasar Sin ya ragu, a cikin wannan mawuyancin hali aka zabi Huang Yubin da ya zama mai horar da 'yan wasa na kungiyar lankwashe jiki ta maza. Bayan shekara daya kuma, Li Yangchun, da Li Jing na kungiyar kasar Sin sun samu lambobin zinariya guda biyu a gasar cin kofin duniya ta lankwashe jiki a karo na 25.
Yanzu, Huang Yubin zai kara shiga wasannin Olympics, bisa matsayinsa na babban mai horar da 'yan wasa na kungiyar lankwashe jiki ta kasar Sin. A lokacin da manema labaru suka yi masa tambaya game da burin kungiyar kasar Sin wajen samun lambobin zinariya, Huang Yubin ya ce,
'Ko za a samu sakamako mai kyau a wasanni, ko a'a, wannan ya danganta kwarewar 'yan wasa, kuma ya danganta da ko 'yan wasa za su iya nuna kwarewarsu sosai a gasar, ko a'a. Mun riga mun nuna kwarewarmu a wasannin cin kofin duniya ta lankwashe jiki na shekarar 2006, da na shekarar 2007. Yanzu kuma muna cigaba da kokarinmu.'
1 2 3 4
|