
Za a yi gasar tseren gudun kananan jiragen ruwa da kwale-kwale na fata da kuma gasar ninkaya ta Marathon a wani yankin ruwa da ke gundumar Shunyi da ke karkarar Beijing. Yanzu 'yan wasa da yawa da suka zo daga kasashe daban daban sun riga sun soma yin aikin horaswa a wannan yankin ruwa. 'Yan wasa da masu horaswa sun bayyana farin cikinsu kan wannan yankin ruwa. Mr. Brett, shugaban kungiyar 'yan wasan tseren kananan jiragen ruwa ya ce, "Lokacin da aka yi gasar cin kofin wasan tseren kananan jiragen ruwa ta kasa da kasa, na taba zuwa wannan wuri. Soba da haka, wannan ne karo na biyu da na zo wannan wuri. Wannan yankin ruwa yana da girma sosai, shi kuma wani kyakkyawan yankin ruwa ne ga wasannin ruwa." (Sanusi Chen) 1 2 3 4
|