
A gun gasar Olympic ta Beijing, wasu dakuna da filayen motsa jiki suna cikin jami'o'i. Alal misali, za a yi gasar wasan kokawa a dakin motsa jiki na jami'ar koyon ilmin aikin gona ta kasar Sin. A cikin wannan dakin motsa jiki da aka gina shi yau da shekara daya da ta gabata, an taba shirya gasar cin kofin wasan kokawa ta matasa ta kasa da kasa.
Mr. Ma Hongfei, wani dalibin da ke karatu a aji na 3 a wannan jami'a. Kamar yadda abokan ajinsa suke yi, shi kuma wani mai aikin sa kai ne ga gasar Olympic ta Beijing. Ya gaya wa wakilinmu cewa, yanzu, ana cikin lokacin gasar Olympic ta Beijing a dakin motsa jiki na jami'ar koyon ilmin aikin gona ta kasar Sin da yankunan da ke kewaya da ita.
"An samu sauye-sauye sosai a jami'armu. Dukkan masu aikin sa kai sun riga sun hau kan mukamansu. A kan titunan da ake bi don shigi da fici a jami'armu, an soma yin bincike kan dukkan motoci bisa bukatar da ake nema a gun gasar Olympic ta Beijing."
1 2 3 4
|